5 बजे - अनुवाद करना

Wani Lauya Yana Zaune A Cikin Jirgi, Sai Wata Kyakkyawar Mace Ta Shigo Ta Zauna A Gefensa.
Bayan Wasu 'Yan Daƙiƙu, Sai Matar Ta Kara Matsowa Kusa Da Shi Tana Magana Da Murya Qasa-Qasa:
Ba Tare Da Ka Jefa Kanka Cikin Wata Matsala Ba, Ka Bani Duk Kuɗaɗen Dake Jikinka …
Idan Ba Haka Ba Zan Yi Ihu Da Qarfi In Ce Kana Kokarin Cin Zarafi Na. Kasan Kuma Idan Nayi Hakan 'Yan Sanda Za Su Zo Su Kama Ka.
*
Lauyan Cikin Nutsuwa Ya Ciro Wata Takarda Ya Rubuta:
Ni Bebe Ne Kuma Kurma, Ba Na Jin Abin Da Kike Faɗa Kuma Ba Na Magana. Don Allah Ki Rubuta Abin Da Kike So A Kan Wannan Takarda.
*
Matar Ta 'Dauki Takarda Ta Rubuta Duk Barazanar Da Ta Faɗa Masa, Ta Miƙa Masa.
Lauyan Ya Karɓi Takardar Ya Sanya Ta Cikin Aljihunsa,
Sannan Ya Ce:
Yanzu Zaki Iya Yin Ihun Ki Yadda Kike So, Shaidar Laifin Da Kika Aikata Ta Na Nan A Cikin Aljihu Na, Kuma Da Rubutun Hannunki!

#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM. CON. MVMech

image